Kai-tsayeKAI-TSAYE
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Takaitacce
Ƙasar Chadi za ta samar da ruwa da wutar lantarki kyauta ga gidaje
'Dakarun Isra'ila sun lakaɗa wa likitoci a Gaza duka sun muzanta su'
Birtaniya na fuskantar ƙarancin ayaba
Rahoto kai-tsaye
Karin bayani
Rahoto kai-tsaye
Daga Habiba Adamu da A'isha Babangida
Birtaniya na fuskantar ƙarancin ayaba👇
An fara fuskantar ƙarancin ayaba a manyan kantunan Birtaniya saboda matsalolin sauyin yanayi da ke tarnaki ga samar da ayabar.
Kwararu sun ce masu son cin Ayaba na fama da tsadarta sakamakon yadda sauyin yanayi ke tasiri kan nomanta a sassan duniya.
Wani mai sharhi kan sha'anin tattalin arzikin ayaba a Majalisar Ɗinkin Duniya, Pascal Liu, ya shaida wa BBC sauyin yanayi na janyo tsaiko da yaɗa cututtukan da ke lalata amfanin gona.
⏯️
Tun a makon da ya wuce ake fuskantar ƙaranci ko rashin ayabar a wasu kantina na ƙasar, bayan guguwar da ta faɗa a tekun Atlantika da ta janyo tsaikon dakon Ayabar ta jirgin ruwa.
Ƙwararru za su yi taro a birnin Rom, domin tattaunawa kan wannan matsala ta ɗaya daga cikin abin da aka fi ciniki da kawo bunƙasar tattalin arziki.


No comments:
Post a Comment