Labarun safiyaryau
_____________________________________________
Matsalar satar mutane masu yawa sosai ta sake kunno kai a Najeriya.
Sau biyu a cikin mako guda, wani gungun ‘yan bindiga da ke kan babura, da suka fito daga dazuka a wurare biyu daban-daban a arewacin kasar, suka yi awon gaba da daruruwan mutane.
Na farko shi ne al'amarin da ya faru a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda mayaka da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka yi awon gaba da mata da yara kanana daga wani sansanin ‘yan gudun hijira a lokacin da suke neman itacen girki.
Sai kuma al'amarin da ya faru da safiyar ranar Alhamis inda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da yara fiye da 280, masu shekaru tsakanin 8 da 15, da kuma wasu malamai daga wata makaranta da ke jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya zuwa wani daji da ke kusa

No comments:
Post a Comment