Dadumi duminsa labarun yau
DA DUMI-DUMI: Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar kawar da wani fitaccen dan ta'adda mai suna Maikusa, Wanda ke rike da matsayi na biyu a cikin 'yan ta'addan dake aiki a jihar Katsina.
DA DUMI-DUMI: Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar kawar da wani fitaccen dan ta'adda mai suna Maikusa, Wanda ke rike da matsayi na biyu a cikin 'yan ta'addan dake aiki a jihar Katsina.
Wannan kungiya dai na karkashin jagorancin fitaccen dan ta'adda da aka fi sani da Modi Modi.
A yayin wani harin da ‘yan ta’addan suka kai a kananan hukumomin Kurfi da Safana na jihar Katsina a Jiya Litinin 4 ga watan Maris 2024, sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’adda inda suka yi nasarar fatattakar Maikusa da wasu ‘yan ta’adda Guda uku. Wannan kazamin farmakin ya kuma kai ga kawar da maboyar 'yan ta'adda a yankin.
A yayin da sojojin ke gudanar da wannan samame sun fuskanci turjiya mai karfi daga ‘yan ta’addan masu tsatsauran ra’ayi amma sun yi jajircewa wajen fatattakar ‘yan ta’addan ta hanyar amfani da makamansu na zamani, lamarin da ya raunana wasu, yayin da wasu suka watse cikin rudani.
Bayan fafatawar, sojojin sun kwato bindigu kirar AK-47 guda biyu, harsashi na musamman 65 mm 7.62,, da kuma kayyakin kariya.
A ci gaba da aikin share fage, sojojin sun kuma kawar da maboyar ‘yan ta’adda a kauyukan Wurma, Shaiskawa, Yauni, da Dogon Marke a karamar hukumar Kurfi, da Ummadau da Zakka a karamar hukumar Safana.

No comments:
Post a Comment