Manyan matsaloli takwas da ke addabar ƴan Afirka ta Kudu gabanin zaɓe
AFP
Bayani kan maƙala
Marubuci,Damian Zane, Dorothy Otieno & Olaniyi Adebimpe
Sanya sunan wanda ya rubuta labari,BBC News
Sa'o'i 3 da suka wuce
Afirka ta Kudu, ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya arziki da tasiri a Afirka, na shirin kaɗa ƙuri'a a zaɓuka na ranar 29 ga watan Mayu yayin da ake fargaba game da rashin aikin yi, da ƙaruwar laifuka, da kuma ɗaukewar lantarki.
A waɗannan tasawirorin, za a ga manyan abubuwan da za su mamaye wannan zaɓe - karo na bakwai ke nan tun bayan fara zangon dimokuraɗiyya a 1994.
Tasawirar da ke nuna goyon bayan da jam'iyyar ANC ke da shi
Bayanan hoto,Tasawirar da ke nuna goyon bayan da jam'iyyar ANC ke da shi
Idan ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ta yi daidai, to lallai za a shiga sabon mataki a fagen siyasar ƙasar.
Jam'iyyar African National Congress (ANC) mai mulki ce ta mamaye fagen siyasar ƙasar tun daga gwagwarmayar da ta yi wajen korar gwamnatin wariya ta fararen fata.
Ta cinye zaɓen farko a 1994 kuma tun daga lokacin take kan mulki.
Amma ƙuri'un da take samua zaɓuka na ci gaba da raguwa tsawon shekaru tun daga 2004, lokacin da ta samu mafi yawan ƙuri'u na kashi 70 cikin 100.
Bincike na nuna cewa za ta iya ƙara raguwa zuwa kashi 50 cikin 100, abin da zai sa ta koma yin haɗin gwiwa.
...
Ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo wa ANC baƙin jini shi ne halin da tattalin arzikin ƙasar ya shiga.
Idan aka duba shekara 30 da suka wuce, 'yan Afirka ta Kudu sun ƙara arziki. Talauci ya ragu, kuma mutane sun samu damar samun gidaje da kuma kiwon lafiya a dunƙule.
Sai dai kuma, an samu raguwar samun kuɗaɗe a adadi na tsakatsaki daga 2011, abin da ya sa wasu da dama kan ji cewa sun ci baya kuma suka fara zargin ANC da yin almubazzaranci da tattalin arzikin ƙasar.
...
Duba adadi na tsakatsaki kawai ba zai ba da cikakken labarin ƙasar ba, saboda akwai bambancin samu tsakanin al'ummomin ƙasar.
Idan aka yi amfani da tsarin da ake kira Gini coefficient, wanda ke duba yawan abin da kowane iyali daga kowane rukuni na al'umma ke samu, za a ga Afirka ta Kudu ce ƙasa mafi rashin daidaito a duniya.
Misali, kashi 20 na al'ummar ƙasar da suka fi arziki su ne ke riƙe da kusan kashi 70 cikin 100 kuɗaɗen da iyalai ke samu. Idan aka kwatanta, sauran kashi 40 mafiya talauci na riƙe ne da kashi 7 cikin 100 kacal na arzikin ƙasar.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
-
News Yadda za ku kula da kanku lokacin azumin Ramadan D Sa'o'i 3 da suka wuce A cikin watan Ramadan mai alfarma, musulmai a sassan ...
-
YANZU YANZU: Kotun kolin ƙasar Saudiyya ta buƙaci al'ummar musulmi su halarci duban jinjirin watan Ramadan a yammacin YANZU YANZU: Kot...
-
Recognizing wisdom and maturity in a person isn’t always about the number of gray hairs on their head. It’s more about observing their beh...
-
Dakarun sojin Isra’ila sun ce sun yi haɗaka da wasu ƙasashe wajen daƙile gomman harin makami mi linzami da Iran ta kai mata. Wannan bayani...
-
Kai-tsayeKAI-TSAYE Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da...
-
Labarun safiyaryau _____________________________________________ Matsalar satar mutane masu yawa sosai ta sake kunno kai a Najeriya. Sau bi...
-
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN 😭 Fitatcen Jarumi kuma Mawaki Yakubu Moh’d ya samu hadarin mota a kan hanyar shi ta zuwa Abuj...
-
A bbc Duk Wanda Ya Fadamana Halin Annabi Guda Daya Allah Yasa Shine Sanadiyyar Shiga Al-jannar Shi . mudai Nace Gaskiya ❤️👇👇👇👇👇👇👇👇...
-
Shiga kakalli full video kabawa mutane labari👇👇👇👇👇👇👇👇👇 Kalli Shagalin Jaruman Kannywood Wanda Suka Hada Dantaya Ali Nuhu Murnar Zam...
-
Innalillahi wa inna ilaihi raji una allah yayi wa mahaifiyar ALASAN KWALLI RASU yanzu yanzu allah ya jiqanta ya gafarta mata...... 👇👇👇...

No comments:
Post a Comment